<description>&lt;p&gt;Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda Najeriya ta gaza samun gurbin alƙalin wasanni a gasar AFCON karo na biyu a jere.&lt;/p&gt; &lt;p&gt;A ƙarshen watan da ya gabata ne hukumar ƙwallon ƙafar Afrika CAF ta fitar da jadawalin alƙalan wasanni da za su bayar da gudunmawa a gasar cin kofin ƙasashen Afrika ta AFCON da zata gudana a Morocco cikin watan gobe, amma ba tare da alƙalin wasa ko guda ɗaya daga Najeriya ba.&lt;/p&gt; &lt;p&gt;Ko a makamanciyar gasar da ta gabata a Ivory Coast cikin shekarar 2024 babu wakilcin ko da alƙalin wasa guda daga Najeriyar, lamarin da ke matsayin babban koma baya ga wannan ƙasa ta tayi shura a fagen ƙwallo.&lt;/p&gt; &lt;p&gt;&lt;em&gt;&lt;strong&gt;Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...&lt;/strong&gt;&lt;/em&gt;&lt;/p&gt;</description>

Wasanni

RFI Hausa

Karo na biyu a jere Alƙalan wasan Najeriya sun gaza samun wakilci a AFCON

NOV 3, 2025-1 MIN
Wasanni

Karo na biyu a jere Alƙalan wasan Najeriya sun gaza samun wakilci a AFCON

NOV 3, 2025-1 MIN

Description

Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda Najeriya ta gaza samun gurbin alƙalin wasanni a gasar AFCON karo na biyu a jere.

A ƙarshen watan da ya gabata ne hukumar ƙwallon ƙafar Afrika CAF ta fitar da jadawalin alƙalan wasanni da za su bayar da gudunmawa a gasar cin kofin ƙasashen Afrika ta AFCON da zata gudana a Morocco cikin watan gobe, amma ba tare da alƙalin wasa ko guda ɗaya daga Najeriya ba.

Ko a makamanciyar gasar da ta gabata a Ivory Coast cikin shekarar 2024 babu wakilcin ko da alƙalin wasa guda daga Najeriyar, lamarin da ke matsayin babban koma baya ga wannan ƙasa ta tayi shura a fagen ƙwallo.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...