Akwai bukatar samarwa masu buƙata ta musamman ayyukan yi domin dogaro da kai

DEC 23, 2025-1 MIN
Ilimi Hasken Rayuwa

Akwai bukatar samarwa masu buƙata ta musamman ayyukan yi domin dogaro da kai

DEC 23, 2025-1 MIN

Description

Mutane da suka tsinci kansu a cikin masu buƙata ta musamman sakamakon nau’ikan nakasar da suka fama da ita sun share shekaru suna fuskantar giɓi babba a muhimman fannonin rayuwa daban daban, ciki kuwa har da samun guraben ayyukan yi ko da kuwa a ce sun yi katarin tsallake shingen samun ilimi, matsalar da ta fi ƙamari a ƙasashe masu tasowa ciki har da na Nahiyar Afrika. Mutane da suka tsinci kansu a cikin masu buƙata ta musamman sakamakon nau’ikan nakasar da suka fama da ita sun share shekaru suna fuskantar giɓi babba a muhimman fannonin rayuwa daban daban, ciki kuwa har da samun guraben ayyukan yi ko da kuwa a ce sun yi katarin tsallake shingen samun ilimi, matsalar da ta fi ƙamari a ƙasashe masu tasowa ciki har da na Nahiyar Afrika. Kan wannan batu shirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan lokaci zai tattauna, bayan da ya yi tattaki zuwa Jihar Jigawa da ke tarayyar Najeriya, akan ƙorafin da wasu fama da nakasar suka yi a bisa ganin cewar suna neman rasa damar samun guraben ayyukan yi da suka cancanci dafewa.   A latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.