Yadda aka yi bikin buɗe gasar cin kofin Afrika ta AFCON a Morocco
DEC 22, 2025-1 MIN
Yadda aka yi bikin buɗe gasar cin kofin Afrika ta AFCON a Morocco
DEC 22, 2025-1 MIN
Description
Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zay yi duba ne kan yadda aka faro gasar lashe kofin nahiyar Afrika da ƙasar Morocco ke karɓar baƙunci. A daren jiya lahadi ne dai aka buɗe gasar lashe ƙofin nahigar Afrika ta AFCON karo na 35 da ƙasar Morocco ke karɓar baƙunci. An dai buga wasanni tsakanin Morocco da Comoros, inda Moroccon ta samu nasasara da ci 2 da nema, wani abu da ke nuna cewa ta faro gasar da ƙafar dama, bayan da Yariya Moulay Hassan bin Mohammed ya buɗe ta tare da rakiyar shugaban hukumar kwallon ƙafa ta duniya FIFA Gianni Infantio da kuma shugaban hukumar kwallon ƙafar Afrika CAF Patrice Motsepe. Ɗan wasan gaba na tawagar Morocco Brahim Diaz da ke bugawa Real Madrid ne ya fara jefa kwallo a raga a minti na 55, kafin Ayoub El Kaabi na ƙungiyar Olympiacos da ya shigo daga baya ya ƙara a minti na 74. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.