Yadda Ragin Farashin Man Fetur Zai Shafi Rayuwar ‘Yan Najeriya

DEC 17, 202515 MIN
Daga Laraba

Yadda Ragin Farashin Man Fetur Zai Shafi Rayuwar ‘Yan Najeriya

DEC 17, 202515 MIN

Description

Rage farashin man fetur a Najeriya na daya daga cikin batutuwan da ke daukar hankalin al’umma, musamman ganin yadda tsadar rayuwa ta yi wa ’yan kasa katutu a ‘yan watannin nan. Man fetur ba wai kawai makamashi ba ne da ake amfani da shi wajen tafiyar da ababen hawa; ginshiki ne da kusan dukkan harkokin tattalin arziki ke jingina da shi – daga sufuri, da samar da kayayyaki, har zuwa rabon su zuwa kasuwanni.Saboda haka, duk wani sauyi a farashin mai kan yi tasiri kai tsaye ko a kaikaice ga farashin kayan masarufi da ’yan Najeriya ke amfani da su a kullum, kamar abinci, da kayan gini, da magunguna da sauransu. Sai dai tambayar da ke yawan fitowa ita ce: shin rage farashin mai zai kai ga rage farashin wadannan kayayyaki? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.